Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan da Amurka sun amince da kammala ayyukan UNAMID a watan Oktoba
2020-05-27 09:35:18        cri

Sudan da Amurka sun amince da kawo karshen ayyukan tawagar MDD mai wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur ko UNAMID a takaice, a watan Oktoban karshen wannan shekara.

Wata sanarwa da majalissar koli ta mulkin Sudan ta fitar ta ce, shugaban majalissar Abdel Fattah al-Burhan, ya zanta ta wayar tarho da mataimakin sakataren wajen Amurka mai lura da harkokin Afirka Tibor Nagy, da wakilin musamman na Amurka a Sudan Donald Booth game da wannan batu.

Sanarwar ta ce Al-Burhan ya amince da ra'ayin jami'an biyu, game da kammala ayyukan tawagar ta UNAMID a watan na Oktoba, ba tare da samar da wata dama ta sake sabunta ayyukan tawagar ba.

Kaza lika sassan biyu sun amince da cewa, tawagar ta kammala ayyukan ta bisa kudirorin ci gaban Sudan, wadanda ke kunshe cikin wata wasika da Sudan din ta aikewa MDD tun a ranar 27 ga watan Fabarairu.

Bugu da kari, shugaban majalissar kolin ta Sudan, ya yi kira ga Amurka da ta kara kaimin tabbatar da goyon bayan shirin kasar sa, na tattauna batun wanzar da zaman lafiyar Sudan dake gudana a birnin Juba, fadar mulkin Sudan ta kudu, ta kuma amince da cire Sudan daga jerin kasashen dake marawa 'yan ta'adda baya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China