![]() |
|
2020-05-20 17:49:00 cri |
Duk da cewa, annobar ta shafi tattalin arzikin duniya da sauran fannoni na rayuwa, wani masanin tattalin arzikin Amurka ya yi amana cewa, managartan manufofin da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar sun tabbatar da saurin farfadowar tattalin arzikin kasar kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata.
Burin dukkanin bil Adama daya ne, wato nasarar yaki da wannan cuta, kuma yin hadin gwiwa shi ne babban makami da muke da shi na kawo karshen wannan matsala da ta gagari kwandila.
Tun bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta ci gaba da gabatarwa duniya muhimman bayanai game da wannan cuta a kan lokaci, kuma ba wata rufa-rufa ba, da ma bayanai kan nazarin da ta yi kan cutar da sakamakon da ta samu, domin yin ma'amala yadda ya kamata da zagowar kasashen duniya. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta hada kai da hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma samar wa kasashen duniya fasahohinta na yin kandagarkin annobar, da yadda likitocin kasar suke ba da jinya ga wadanda suka kamu da cutar.
Baya ga sanar da WHO da sauran kasashe matakai da dabarun yaki da wannan annoba, kasar Sin ta tura tawagogin ma'aikatan lafiya da kayayyakin kiwon lafiya zuwa kasashe daban-daban na duniya ciki har da aminanta kasashen Afirka don taimakawa kokarin kasashen na yaki da COVID-19, hakan ya kara tabbatar da zumunci da aniyar kasar Sin na yin hadin gwiwa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.
Sanin kowa ne cewa, babu wanda shi kadai zai iya kare kansa daga wannan mummunar cuta mai yaduwa, kana, a halin yanzu, babu wata kasa da za ta iya kare kanta ba tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen ba. Yakin da muke yi da cutar numfashi ta COVID-19 ya kasance yakin da dukkanin bil Adma ke yi da cutar, ba za mu iya cimma nasarar yaki da wannan annoba ba, in babu hadin gwiwar kasa da kasa. Haka kuma yunkurin wasu mutane ko kasashe na siyasantar da batun yaki da cutar, za su kawo illa ga hadin gwiwar kasashen duniya na yaki da wannnan annoba da a halin yanzu ta dakatar da komai a duniya.
Masana kiwon lafiya sun sha bayyana cewa, har yanzu babu wanda ya san asalin wannan annoba, kuma ba ta da magani. Don haka, duk wasu kalamai marasa tushe na nuna kiyayya ko neman shafawa wata kasa bakin fenti game da wannan cuta, ba komai ba ne illa neman cimma wani buri na siyasa. Kuma hakan babu abin da zai haifar, face mayar da hannu agogo baya. Abu mafi muhimmanci a wannan lokaci, shi ne yin hadin gwiwa don fuskantar wannan matsala, ta yadda za mu gina makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama. Annobar COVID-19, tamkar wani muhimmin darasi ne da duniya baki daya ta koya. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China