Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta kaddamar da sabbin dabarun zurfafa hidimomin kudi ta yadda kowa zai amfana
2020-05-19 10:32:59        cri

Ghana ta kaddamar da wasu sabbin dabaru 3 dake da nufin kara zurfafa bada hidimomin kudi, ta yadda kowa zai ci gajiya, domin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.

Daga cikin dabarun 3, akwai dabarar raya hidimomin da suka shafi kudi ta kasa da za ta amfanawa kowa, wadda aka samar da hadin gwiwar Bankin Duniya, da nufin kara samar da hidimomin kudi ga jama'a, daga kaso 58 zuwa 85 ya zuwa shekarar 2023, da kuma samar da damarmakin samun kudin shiga da nufin rage fatara.

Ghana ta kuma samu taimako daga shirin kawancen kasashe da hukumomi na MDD wato Better-Than-Cash Alliance, wanda ke rajin sauya tsarin amfani da tsabar kudi zuwa ta hanyoyin fasaha na zamani.

Shirin kawancen zai taimakawa Ghana samar da tsarin da ake kira Cash-Lite, wanda ke da nufin samar da tsarin biyan kudi ta fasahohin zamani da kyautata hidimomin da suka shafi kudi, da bada damar sa ido kan hada-hadar kudi da kuma kare hakkin masu amfani da hidimomin.

Ministan kudi na kasar Ken Ofori-Atta, ya ce janyewa daga amfani da tsabar kudi zai taimakawa kasar samun damar cimma muradun ci gaba masu dorewa da dama.

Manajan Daraktan shirin Better-Than-Cash Alliance, Ruth Goodwin-Groen, ta ce Ghana ta riga ta samu nasara a fannin biyan kudi ta fasahohin zamani. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China