Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kafofin watsa labaran kasa da kasa sun soki tsokacin Pompeo
2020-05-16 16:44:49        cri
Manyan kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasar Amurka, sun dauki matakai iri guda wajen sukar sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo.

A karshen watan Aflilun da ya gabata, sau biyar babban rukunin gidajen rediyo da telibiji na kasar Sin wato CMG ya soki matakan da Pompeo ya dauka domin shafawa kasar Sin bakin fenti a cikin shirinsa na CCTV News, a sa'i daya kuma, manyan kafofin watsa labarai na Amurka, ciki har da CNN, su ma sun gabatar da sharhin na CCTV News, inda suka soki tsokacin Pompeo.

Daga tsokacin da Pompeo ya fitar a fili a kan shafin intanet na gwamnatin Amurka, an lura cewa, kaso 80 bisa dari dake cikin tsokacin zargi ne da ya yi wa kasar Sin, misali "asalin kwayar cutar COVID-19" da "yunkurin boye yanayin yaduwar cutar na kasar Sin" da kuma "laifin kasar Sin na barkewar annobar", a takaice dai yana son dora laifin gwamnatin Amurka na gazawa wajen daukar matakan da suka dace na dakile annobar ta hanyar shafawa kasar Sin bakin fenti.

Alkaluman da cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da sauran kasashen duniya ta hukumar CIPG wato rukunin wallafa litattafan harsunan waje ta fitar, sun nuna cewa, yawancin manyan kafofin watsa labaran kasa da kasa sun soki tsokacin Pompeo, ban da wasu cikin su da suka wallafa tsokacin nasa kai tsaye.

A cikin kafofin watsa labarai na Amurka, jaridar Washington Post da CNN da shafin intanet na Politico, sun fi nuna rinjaye a bangaren, inda kwararrun likitoci da jami'an gwamnati da masu fashin baki suka nuna rashin amincewa tare da sukar tsokacin na Pompeo.

Jaridar The Hill ta Amurka ta taba wallafa wani rahoto mai taken "Pompeo, karen Trump wanda ya zargi kasar Sin bisa barkewar cutar COVID-19 ", inda aka tattara sukar da bangarori daban daban suka yi wa Pompeo. Har ila yau, a ranar 17 ga watan Aflilu, jaridar New York Times ta fitar da wani rahoto, inda aka bayyana cewa, "Cikin sauki aka gano matakin da jam'iyyar Republic ta dauka, wato yunkurinta shi ne dora laifi kan kasar Sin, ta yadda za ta boye hakikanin yanayin da kasar ke ciki na gaza dakile annobar COVID-19."

Yanzu annobar tana ci gaba da yaduwa cikin sauri a Amurka, amma bisa matsayinsa na sakataren harkokin wajen kasar, Pompeo bai kula da kiyaye rayukan al'ummun kasar ba, inda yake neman dorawa wasu laifi. ko shakka babu hakan ya bata sunan Amurka, har da lahanta amincin kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China