![]() |
|
2020-05-15 19:27:39 cri |
Da yake karin haske yayin taron manema labarai da hukumar ta kira Jumma'ar nan, ya ce ya zuwa yanzu, ba a samu wasu manyan matsaloli a gwajin farko na alluran rigakafin cutar da aka yi ba.
Daga cikin alluran riga kafin da ake gwajin nasu, sun hada da adenovirus vecrot da wasu alluran guda hudu da hukumar kula da magunguna ta kasar Sin take bin diddiginsu.
Zeng ya ce, masu aikin sa-kai 2,036 ne suka amince a gwada kashi na biyu na alluran rigakafin a jikinsu, kuma masu bincike na tantance ko riga kafin ba shi da hadari yana kuma aiki, ko akasin haka.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China