Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dan Jaridar Nijeriya: bai dace a nemi diyya daga kasar Sin ba
2020-05-13 13:42:15        cri
Dr. Austin Maho, gogaggen dan jarida a Nijeriya, ya wallafa wani sharhi mai taken "mafarkin Oby Ezekwesili" a kafar yada labarai ta yanar gizo ta "Daybreak" dake kasar, inda ya jaddada cewa, ikirarin tsohuwar ministar ilimi ta kasar, kuma tsohuwar mataimakiyar shugaban bankin duniya, Oby Ezekwesili, na neman diyya daga kasar Sin, ba shi da gurbi bisa doron doka da kuma hankali, kuma abu ne mai wuya ya samu goyon baya.

Sharhin ya nuna cewa, kokarin kasar Sin na yaki da annobar COVID-19 a bayyane yake ga kowa, inda ya ce, al'ummomin kasa da kasa, ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO, sun yabawa kasar Sin, hatta shugaban Amurka Donald Trump, ya fito ya yaba mata.

Ya kara da cewa, Oby Ezekwesili na son gabatar da kanta a matsayin mai kare nahiyar Afrika, amma muradun kasashen yamma kawai take karewa. Ya ce a lokaci mai muhimmanci na yaki da COVID-19, ta bukaci kasashen Afrika su nemi diyya daga kasar Sin, wadda ita ma tasirin cutar ya shafe ta.

Ya ce cikin shekaru 20 da suka gabata, dangantakar Sin da Afrika ta haifar da kyawawan sakamako. Kuma abun da Afrika ke bukata a yanzu shi ne, karfafa dangantaka da kasar Sin, maimakon neman diyya daga wajenta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China