Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridun Nijeriya sun wallafa sharhin da Jakadan kasar Sin da ke tarayyar Nijeriya ya bayar
2020-05-12 15:42:24        cri






A jiya Litinin, jaridun This Day, da Daily Trust, da The Guardian da sauransu, sun wallafa sharhin da jakadan kasar Sin da ke tarayyar Nijeriya, Mr.Zhou Pingjian ya rubuta, wanda ke da taken "hada kan juna don shawo kan cutar COVID-19".

A sharhin da ya bayar, Ambasada Zhou Pingjian ya ce, "Mr. Echar Christopher Sunday, dan kasuwar Nijeriya gaskiya jakada ne da ke sada zumunta a tsakanin kasarsu da kasar Sin. Labarinsa da jaridar China Daily ta wallafa a ranar 6 ga wata gaskiya ya sosa mini rai."

Ambasada Zhou Pingjian ya kara da cewa, Mr.Echar ya shafe sama da shekaru 10 yana rayuwa a lardin Guangdong na kasar Sin, wanda a watan Maris na bana ya amsa kirar mahukuntan wurin, kuma bisa taimakon uwar gidansa 'yar kasar Sin, ya zama mai aikin sa kai wajen yaki da cutar COVID-19.

Akwai baki sama da 1900 da ke rayuwa a birnin Zhanjiang na lardin Guangdong, kuma Mr. Echar ya zama daya daga cikin rukuni na farko na masu aikin sa kai da ke samar da hidimomi ga baki ta fannin yaki da cutar. Wadannan masu aikin sa kai sun iya Turancin Ingilishi, da Japananci, da Faransanci, da harsunan Spaniya da Koriya.

Echar ya ce, Zhanjiang gidansa ne na biyu, don haka ya yi farin ciki da ba da taimakonsa ga birnin. Bisa horaswar da aka yi musu, Mr. Echar ya fara aikin auna zafin jikin baki da suka sauka a filin jirgin sama na Zhanjiang, da kuma fadakar da su kan harkokin kandagarkin cutar. Bayan ya jima yana wannan aiki, ya gano cewa, wasu baki ba su fahimci muhimmancin aikin gwajin cutar ba, kuma a ganinsa ziyartarsu a unguwannin da suke zama, zai iya kara fadakar da bakin game da matakan kandagarkin cutar. Don haka, ya fara ziyartar baki da ke rayuwa a unguwanni daban daban tare da uwar gidansa, don taimakawa baki 'yan kasashen Afirka fahimtar matakan da aka dauka na kandagarkin cutar, kuma kokarin da ya yi ya kuma taimaka ga inganta mu'amala da cudanya da su.

Ambasada Zhou Pingjian ya ce, ina fatan Allah ya hada ni da Mr. Echar da uwar gidansa 'yar kasar Sin, da kuma 'ya'yansu guda biyu wata rana. A hakika ba safai ake samun 'yan Nijeriya irinsu Echar da ke kokarin sada zumunta a lardin Guangdong.

Ambasada Zhou Pingjian ya ci gaba da cewa, "zan so in bayyana godiya ga jakadan tarayyar Nijeriya da ke kasar Sin, Baba Ahmad Jidda. " Ya ce, Ambasadan ya koma birnin Beijing a ranar 8 ga watan Afrilu, kafin daga bisani a killace shi har tsawon kwanaki 14 a birnin Taiyuan, a sakamakon yadda a lokacin aka bukace jiragen da ke zirga-zirga a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya su sauka a sauran birane, don a duba lafiyar fasinjojinsu, kafin daga bisani su sauka a birnin Beijing. Babu shakka, yadda aka killace shi a birnin Taiyuan babu dadi, sai dai Ambasada Baba Ahmad Jidda ya ce, "Ya kamata kowa ya bi dokar da aka kafa, domin kare lafiyar kowa da kowa."

Ambasada Zhou Pingjian ya ce, kasancewarta kasar da ke cikin kasashen farko da cutar COVID-19 ta fara addabarsu, kasar Sin ta fi saurin shawo kan yaduwar cutar, kuma hakan ya faru ne a sakamakon yadda kasar Sin ta dauki kwararan matakai masu inganci, duk da cewa an yi miyagun hasarori, amma matakan na da amfani.

Ya ce , a ranar 23 ga watan Janairu, an kulle birnin Wuhan, kuma a ranar 8 ga watan Afrilu, an soke haramcin tafiye-tafiye da aka saka a birnin, bayan da ya shafe tsawon kwanaki 76 a rufe.

Ya zuwa ranar 26 ga watan Afrilun kuma, an sallami dukkan masu cutar da ke kwance a asibiti bayan da suka warke. A yayin da ake fama da cutar, an dakatar da zirga-zirgar mazauna birnin, wadanda suka zauna a gida ba tare da fita ba, wadanda kuma suka taimaka ga rage saurin yaduwar cutar.

Ambasada Zhou Pingjian ya kara da cewa, "Abin da ya faru a lardin Guangdong a kwanan baya kusan ya zama iri daya ne da na Wuhan. Sabo da shawo kan cutar ne aka dauki matakan, kuma ba wai sabo da 'yan Nijeriya ko 'yan Afirka, ko kuma bakin da suka zo daga wata kasa ne ake daukar matakan ba.

Daga ranar 5 zuwa 23 ga watan Afrilun, gaba daya akwai baki 138,700 da aka yi wa gwaji, ciki har da 'yan kasashen Afirka 5503, daga cikinsu kuma an gano 185 da suka harbu da cutar, kuma 164 daga cikinsu ba su nuna ko alamar kamuwa da cutar ba. Hadin kan da suka bayar da kuma sadarkarwarsu ya taimaka ga kiyaye lafiyar kowa da ke rayuwa a wurin."

Ambasada Zhou Pingjian ya ce, a game da matsalolin da suka shafi 'yan Nijeriya a yayin yaki da cutar, mahukuntan lardin Guangdong na matukar mai da muhimmanci a kai, kuma sun gaggauta bincike tare da inganta ayyukan da ake aiwatarwa. Ya zuwa ranar 7 ga wata, an daidaita dukkanin koke-koke 26 da aka gabatar yadda ya kamata. Ya ce, ni kaina na duba koke-koken, kuma na gano cewa rashin fahimta ne, a sanadin rashin mu'amala da juna yadda ya kamata ya haifar da matsalar.

Jakadan ya jaddada cewa, muna godiya ga aminan mu 'yan Nijeriya da suka hada kan su da mu wajen tinkarar wahalhalun. Gwamnatin kasar Sin na daukar matakai na bai daya a kan dukkanin baki da ke kasar Sin, kuma ba ta yarda da nuna bambanci ga wasu ba, kuma ko kadan ba za ta kawar da kai ga kalamai na nuna bambanci ba. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China