![]() |
| 2020-05-11 14:58:56 cri |

A matsayin uwa, kwanciyar hanakli da farincikin danta, shi ne kwanciyar hankalinta. A wajen mahaifiyar Xi Jinping, Qi Xin, yana da nauyin da ya rataya a wuyansa, nauyin kasa da al'ummarta. Kalamai da dabi'un mahaifiyarsa sun koya masa yanayin zaman rayuwa.
Madam Qi Xin, ta kasance mai rayuwa cikin sauki, ba ta nuna bambanci a tsakaninta da jama'a. Tsarin iyalinsu shi ne karatu da aiki tukuru. Duk gajiyar da Madam Qi Xin za ta yi, ta kan nace wajen mayar da hankali ga aikinta kuma ba ta jinkirta yin shi. A kullum, mahaifiya kan zama abun misali, inda su kan yi tasiri wajen koyar da 'ya'yansu kyakkyawan tsarin zaman iyali, kuma Xi Jinping, wanda tsarin iyalinsa ya yi matukar tasiri a kansa, na koyi da irin wadancan dabi'u.

A lokacin da Xi Jinping ya tafi aiki a yankunan karkara a arewacin Shaanxi, mahaifiyarsa ta ba shi kyautar da aka saka da hannu, dake dauke da kalmomi cikin jan launi: Zuciyar Uwa!

A lokacin zamansa a Liang Jia He, Xi Jinping bai bata kunya ba. Bayan shekaru 7 yana rayuwa a kauye, ya kulla aminci mai karfi da al'ummar arewacin Shaanxi.

Yayin bikin bazara na shekarar 2001, Madam Qi Xin ta buga wa Xi Jinping waya, a lokacin yana gwamnan Lardin Fujian. A wannan lokaci, Xi Jinping bai zo birnin Beijing don haduwa da iyalinsa ba.

Da ta ji cewa danta ba zai iya zuwa gida ba saboda aiki, Qi Xin murna ta yi. Ta ce "muddin kana aikinka da kyau, girmamawa ce ga iyaye. Wannan alhaki ne dake kanka da kuma iyalinka. Duk daya ne"
A ofishin Xi Jinping, akwai wasu hotunan iyalinsa a ko da yaushe. Daya daga cikin hotunan an dauke shi ne lokacin da suka fita shan iska da mahaifiyarsa. Xi Jinping na matukar girmama mahaifiyarsa. Wani lokaci bayan sun gama cin abincin dare, Xi Jinping kan rike hannunta su fita mike kafa da kuma hira. (By Fa'iza Mustapha daga CRI Hausa)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China