2020-05-08 11:54:32 cri |
Yayin da ake fama da yaduwar cutar COVID-19 a kasashe daban daban, kasar Sin ta riga ta samu ci gaba sosai a fannin hana yaduwar cutar a cikin gidanta. To, wadanne dabaru kasar Sin ta dauka ta yadda har ta kai ga samun wannan ci gaba?
Cutar COVID-19 wata babbar barazana ce da daukacin bil Adama ke fuskanta tare. Kasar Sin kasa ce da ta fara sanar da bullar annobar, gami da daukar matakan dakile yaduwar cutar. Bisa hadin gwiwar da jama'ar kasar suke yi, gami da wahalhalun da suka haye, kasar ta zama ta farko wadda ta samu damar shawo kan yaduwar cutar cikin kasashen duniya. Ta wannan hanya, ta taimakawa kokarin hana yaduwar cutar COVID-19 a duniya, tare da samar da dimbin fasahohi masu amfani ta fuskar aikin dakile cutar.
Cikin fasahohin kasar Sin, da dabarun da ta dauka don dakile yaduwar cutar COVID-19, akwai hadin gwiwar sassa daban daban na kasar a kokarin daukar matakan kandagarkin cuta. Misali, lokacin da aka fara samun labarin barkewar cutar, shugaban kasar, mista Xi Jinping, da kansa ya jagoranci wasu tarukan manyan kusoshin kasar don tabbatar da cikakkun matakan da za a dauka don tinkarar annobar. Ban da wannan kuma, birnin Wuhan, inda annobar ta fara barkewa a cikin kasar Sin, ya katse hanyoyin da suka hada shi da sauran wuraren kasar, inda mutanen birnin kimanin miliyan 9 suka yi kokarin killace kansu a gida, har tsawon kwanaki 76. Sa'an nan, likitoci dubu 42 sun shiga cikin birnin Wuhan, daga wurare daban daban na kasar, don taimakawa aikin ceton rayukan majiyyata a can. Inda har aka gina wasu manyan asibitocin kula da masu kamuwa da cutar COVID-19 guda 2, ko wanensu cikin wasu kwanaki 10.
Sa'an nan cikin dalilan da suka sa aka iya shawo kan cutar COVID-19 a kasar Sin, akwai hakuri da jajircewa da jama'ar kasar suka nuna. Zuwa yanzu wasu mutane 4643 sun rasa rayuka a cikin kasar, sakamakon cutar COVID-19. Cikinsu har da wasu likitoci 23, wadanda suka sadaukar da rayukansu don ceton mutane. Ban da haka, kasar ta dakatar da ayyukan tattalin arziki, tare da kaddamar da matakan kandagarkin annoba cikin gaggawa a daukacin wuraren kasar. Inda jama'ar kasar suka yi kokarin killace kansu a gida har na wasu makonni, haka zalika, an dauki sauran matakan da suka hada da takaita zirga-zirga, da binciken zafin jikin mutum a ko ina na kasar, da tilasta sanya marufin baki da hanci, da dai sauransu. Irin jajircewar da Sinawa suka nuna ta sa Antonio Guterres, sakatare janar na MDD, ya yaba musu, tare da cewar "Sinawa sun sadaukar da salon zamansu na yau da kullum don tinkarar annoba, inda suke samar da babbar gudunmowa ga daukacin bil Adama."
Haka zalika, dabarun da kasar Sin ta dauka a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 sun hada da kokarin hadin gwiwa da kasashe daban daban. Kasar ta fara sanar da yanayin cutar ga hukumar lafiya ta duniya WHO a kai a kai, tun daga ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2019, wata daya gabanin hukumar ta fara bayyana cutar a matsayin "annobar da ya kamata kasa da kasa su lura da ita". Sa'an nan a lokacin da ake kokarin yaki da cutar a kasashe daban daban, kasar Sin ta tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashe daban daban, gami da jigilar kayayyakin kandagarkin cutar zuwa wurare daban daban na duniya wadanda ke da bukata. Haka zalika, kasar Sin tana ta kokarin sabunta bayanai game da fasahohin kula da majiyyata masu cutar COVID-19, tare da raba bayanan ga dukkan kasashen duniya.
Dalilin da ya sa kasar ta yi haka, shi ne domin ta san cewa, kwayoyin cuta ba su san kan iyakar kasa ba, don haka ba za a samu damar kawo karshen aikin dakile cutar ba, muddin akwai wani wuri a duniya dake ci gaba da fama da cutar. Don haka kasar Sin na son sauke nauyin dake bisa wuyanta, don hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin kare lafiyar jama'ar duk duniya. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China