![]() |
|
2020-05-08 10:10:32 cri |
Guterres ya bayyana goyon bayansa ga sabuwar gwamnatin, kana ya bukaci a aiwatar da muhimman sauye-sauye wadanda za su inganta zaman rayuwar al'umma da bunkasa ci gaban tsarin demokaradiyyar kasar Iraki, kamar yadda kakakin sakataren MDDr Stephane Dujarric, ya fada cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, Mista Guterres ya jaddada muhimmancin aiwatar da manufofin da za su biya muradun jama'ar Iraki ta hanyar matakan siyasa inda za'a baiwa mata da matasa damammakin shiga a dama da su, har ma da kananan kabilu da mabiya addinai.
Sakatare-janar na MDDr ya bada gwarin gwiwar kammala kafa gwamnatin hadakar wacce za'a baiwa mata mukamai a majalisar zartaswar kasar domin cike gibin da har yanzu ake da su. Haka zalika, ya jaddada aniyar MDD wajen goyon bayan al'ummar Iraki da gwamnatin kasar a kokarin da suke na yaki da annobar COVID-19 da kokarin cimma nasarar shirin samar da dawwaumammen ci gaban kasar. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China