Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya ba da umarnin kara azama wajen gano masu dauke da cutar COVID - 19
2020-05-07 20:59:19        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a kara azama, wajen shawo kan manyan kalubale da ake fuskanta, tare da inganta dabarun zamani, na gano masu dauke da cutar COVID a sassan kasar.

Li Keqiang, ya yi wannan kira ne yayin da yake shugabantar taron tawagar koli, mai lura da yakin da kasar ke yi da wannan annoba. Taron ya kuma yi nuni da cewa, da zarar an gano bullar cutar a wani wuri, ya zama wajibi a gaggauta shawo kan ta, a bibiyi shaidun ta, a kuma fitar da bayanai a fili ba tare da wata rufa rufa ba. Kaza lika a kauracewa boye wani abu, ko rage wata shaida mai nasaba da hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China