![]() |
|
2020-05-06 22:00:15 cri |
Hakika, kafin wannan furuci na Michael Melham, tuni shugaban cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Amurka Robert Redfield ya bayyana a fili cewa, wasu da suka mutu a yayin yaduwar cutar mura a watan Satumbar bara, a hakika cutar COVID-19 ce ta kama su. Abun tambaya a nan shi ne, mutane nawa ne aka yi zaton sun kamu da cutar? Kuma a hakika sun mutu ne sakamakon cutar COVID-19. Ko tun a watan Satumbar bara ne cutar COVID-19 ta fara yaduwa a tsakanin unguwannin kasar?.
Baya ga haka, a karshen watan Faburairu, fadar White Housa ta nemi jami'an kasar, da sassan lafiya, da ma masanan da abin ya shafa, da su samu amincewa daga ofishin mataimakin shugaban kasar kafin su yi wani furuci a fili game da annobar. Sai kuma ya zuwa ranar 2 ga watan Maris, cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar ta daina samar da alkaluman da suka shafi mutanen da aka yi wa gwaji, da kuma wadanda suka mutu sakamakon cutar, bisa dalili na wai alkaluman ba su yi daidai ba. A sakamakon gazawar gwamnati kuma, har yanzu wata jami'ar kasar ce ke kula da aikin kididdigar.
'Yan siyasar Washington sun yi ta boye yanayin cutar da kasar ke ciki, tare da lalata kokarin da ake yi na yaki da cutar, don neman boye gazawarsu wajen gudanar da harkokin mulki. Hakan kuma ya bayyana dalilin da ya sa cutar ke ta yaduwa a kasar dake kan gaba a duniya ta fannin kiwon lafiya da fasahohin kimiyya.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China