![]() |
|
2020-05-03 15:59:53 cri |
A cewar Afrika CDC, yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a nahiyar Afrika ya kai 1,689 ya zuwa ranar Asabar.
Alkaluman cibiyar ta Africa CDC sun nuna cewa kasashen da annobar COVID-19 ta fi yin kamari a nahiyar Afrika sun hada da Masar, Afrika ta kudu, Morocco da Algeria.
Africa CDC ta ce, shiyyar arewacin Afrika ne annobar COVID-19 ta fi yiwa illa a fadin nahiyar wanda ya hada da yawan mutanen da suka kamu da cutar da kuma mutanen da cutar ta kashe.
Tun da farko a wannan makon, Africa CDC ta karbi kashi na uku na gudunmowar kayayyakin kiwon lafiya daga gidauniyar attajirin kasar Sin Jack Ma da Alibaba domin taimakwa kasashen wajen yaki da annobar COVID-19. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China