![]() |
|
2020-05-02 17:04:23 cri |
Ministan lafiya na kasar Zweli Mkhize, ya bayyana a jiya cewa, an samu sabbin mace-macen ne a lardunan yammacin da gabashin Cape da Guateng da KwaZulu Natal.
Ya ce la'akari da matakin da suka dauka na bada rahoton mace-macen da kadai aka tabbatar, akwai jinkiri wajen tantancewa da tabbatar da wasu daga cikin rahotannin.
Ya zuwa jiya Juma'a, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 5,951, yayin da 2,382 suka warke a kasar Afrika ta kudu. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China