Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harkokin sarrafa kayayyaki a Amurka ya yi kasa
2020-05-02 16:40:18        cri
Cibiyar nazarin ayyukan samar da kayayyaki ta Amurka, ta ce harkokin tattalin arziki a bangaren sarrafa kayayyaki na kasar, sun yi durkushewar da ba a taba gani ba cikin shekaru 11 da suka gabata, biyo bayan barkewar annobar COVID-19 da kuma faduwar kasuwar makamashi ta duniya.

An samu raguwar ne biyo bayan rahoton da ma'aikatar cinikayya ta kasar ta fitar, da ya nuna cewa cikin rubu'i na farko na bana, yawan sarrafa kayayyaki da bada hidima a kasar, ya sauka da kaso 4.8, wanda shi ne mafi muni da aka gani tun bayan matsalar kudi da aka shiga a shekarar 2008. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China