Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun karbi tallafi kashi na uku daga gidauniyar Jack Ma da Alibaba
2020-04-29 10:52:28        cri
Cibiyar dakile yaduwa da kandagarkin cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, ta karbi kaso na uku na dimbin kayayyakin kiwon lafiya, daga gidauniyar attajirin nan dan kasar Sin wato Jack Ma, da gidauniyar Alibaba, a matsayin karin tallafi ga Afirka, a gabar da nahiyar ke ci gaba da yaki da bazuwar cutar COVID-19.

Kamfanin jiragen sama na Ethiopia ne ya yi jigilar wannan kashi na kayan tallafi, wanda ya isa filin jiragen sama na kasar Habasha a ranar Litinin. Kayayyakin sun kunshi marufin baki da hanci miliyan 4.6, da tsinken daukar samfur daga jikin mutane da sinadaran gwaji guda 500,000, da na'urorin tallafawa numfashi 300, sai kuma rigunan kariya na jami'an lafiya 200,000, da gilasan kare fuska 200,000.

Sauran sun hada da na'urorin gwada zafin jiki na hannu 2,000, da manyan na'urorin gwada zafin jiki 100, da safar hannu 500,000. Ana kuma fatan samun karin tallafi na irin wadannan kayayyaki cikin kwanaki masu zuwa.

Da yake bayyana godiyar sa game da wannan taimako ta wani sakon Tiwita da ya wallafa, firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya jinjinawa gidauniyar Jack Ma da Alibaba, bisa ci gaba da goyon bayan da suke nunawa nahiyar Afirka musamman a wannan yanayi da ake ciki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China