Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin: Za a kara taimakawa kamfanonin kasashen waje
2020-04-28 19:19:35        cri
Rahotanni daga ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin a yau Talata sun nuna cewa, an gudanar da wasu gwaje-gwajen ayyuka a yankunan ciniki cikin 'yanci na gwaji dake lardunan Guangdong, da Tianjin, da Fujian, inda aka kirkiro wasu sabbin tsare-tsaren gudanar da ayyuka guda 105, wadanda ake kokarin yada su zuwa sauran sassan kasar.

A nashi bangare, Tang Wenhong, darekta mai kula da tashoshin jiragen ruwa dake cikin yankunan ciniki maras shinge karkashin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya ce za a kara kokarin aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje a yankunan ciniki maras shinge, tare da samar da karin tallafi ga kamfanonin kasashen waje dake kasar ta Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China