Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
SOS! Dole ne a share fage sosai don ba da kariya ga Afirka daga cutar COVID-19
2020-04-28 13:57:50        cri

Yanzu haka cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a sassan Afirka, nahiyar da ba ta da kwarewa a fannin binciken lafiya ba, kuma kasashen ta ba su da tsarin kiwon lafiya mai inganci, ga kuma karancin albarkatu, baya ga fama da bala'in farin dango da cutar malariya da wasu sassan nahiyar ke yi.

Idan aka gaza dakile yaduwar cutar COVID-19 yadda ya kamata, to cutar za ta haddasa matsalar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da tsaron lafiya da ma jin kai. Don haka dole ne a share fage sosai don kare Afirka daga cutar, kuma babu yadda za a yi sai kasashen duniya sun mara mata baya sosai.

Kasancewar nahiyar Afirka ba ta da kwarewa sosai wajen binciken ganon kwayoyin cutar COVID-19, hakan ya sa alkaluman mutanen da ake bayyanawa sun kamu da cutar suke yin kasa da wadanda ke dauke da ita.

Domin sake tantance halin fama da cutar da Afirka ke ciki, cibiyar shawo kan cututtukan Afirka ta tsai da kudurin kaddamar da aikin binciken ganon kwayoyin cutar sau miliyan daya cikin wata guda, yayin da ake sa ran kammala binciken sau miliyan goma cikin watanni hudu masu zuwa.

Amma Furofesa Evaristus Irandu na Jami'ar Nairobi ta Kenya, yana ganin cewa, tsarin kiwon lafiya na Afirka da ba ya iya aiki yadda ya kamata, ba zai iya samar da isasshen goyon baya wajen dakile yaduwar cutar, da ma ceton masu kamuwa da cutar. Don haka ko da ana kyautata kwarewar Afirka wajen binciken kwayoyin cutar, da ma kara yawan mutanen da za a yi musu binciken, amma dakile cutar da ma ceton wadanda cutar ta harba aiki ne mai matukar wuya.

Bisa wani rahoton da kungiyar WHO ta fitar a farkon watan nan da muke ciki, an ce, yawan gadajen da ke sassan gobe da nisa wato ICU da ake iya amfani da su wajen yaki da cutar COVID-19 ba su kai 5000 ba, wato ko wadanne 'yan Afirka miliyan daya na iya samun gadajen biyar kacal. Ban da wannan kuma, yawan na'urorin numfashi da kasashen Afirka 41 ke da su ba su zarce 2000 ba.

Bugu da kari, kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD ya yi gargadi a tsakiyar watan nan, cewar sakamakon rashin ingancin tsarin kiwon lafiya na Afirka da ma karancin kudi, kuma idan aka gaza takaita yaduwar cutar a nahiyar, a yanayi mafi kazanta, cutar za ta harbi mutane kimanin biliyan 1.2, yayin da miliyan 3.3 za su mutu. A yanayi mafi kyau kuma, mutane miliyan 122 za su kamu da cutar, yayin da dubu 300 za su mutu.

Cutar ba ta iya bambanta kasashe da ma kabilu, kalubale ce da ke gaban bil Adama gaba daya. Kaza lika ba za a iya kawo karshenta ba, har sai kasashen duniya sun hada kansu sosai.

Kasashen Afirka ba su da isasshen karfi na tinkarar cutar COVID-19, suna kuma gaggauta bukatar yawan hannu daga kasashen duniya a fannonin kudi, fasaha, kayayyaki, da ma na'urori, a kokarin kyautata kwarewarta ta yaki da cutar.

Bikin magaji ba ya hana na magajiya. Yayin da kasar Sin ke kokarin dakile yaduwar cutar a cikin gida, tana ta samar da taimako ga Afirka ba tare da bata lokaci ba, kamar samar da kayayyakin yaki da cutar, da tura kwararrun likitanci, da ma more fasahohin yaki da cutar.

A ranar 23 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta sanar da kara samar wa WHO kudin taimako har dala miliyan 30 domin yaki da cutar, domin mara wa kasashe masu tasowa baya a fannin raya tsare-tsaren kiwon lafiya. Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya taba bayyana cewa, "A wannan muhimmin lokaci na yaki da cutar COVID-19 na duk duniya, goyon bayan WHO shi ne goyon bayan manufofi, da ka'idojin ra'ayin cudanyar bangarori da dama, da ma kiyaye matsayi da kwarjikin MDD."

Babban magatakardan MDD António Guterres ya taba furta cewa, cutar COVID-19 ba matsalar kiwon lafiya kadai ba ce, babbar matsala ce ga dukkan bil Adama. Annobar ba yaduwar kwayoyin cuta kawai ba ce, domin kuwa za ta haddasa karuwar yawan masu rashin ayyukan yi, da matsalar jin kai. "A gaban wannan sabon kalubalen da ba a taba ganin irinsa a baya ba, shin kasa da kasa za su iya daukar matakai tare da Afirka ko a'a, hakan zai kansace jarrabawa mafi muhimmanci ga hadin kan duniya."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China