![]() |
|
2020-04-21 16:06:36 cri |
A kwanakin baya, an dawo da tafiye-tafiyen jiragen kasa masu jigilar kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. A ranar 7 ga wata, kasar Sin ta tsai da kudurin kafa yankunan gwajin kasuwanci 46 tsakanin kasa da kasa ta yanar gizo, tare da yankuna 59 da aka riga aka zartas da kafawarsu a baya, gaba daya, za a samu yankunan gwajin kasuwanci ta yanar gizo a tsakanin kasa da kasa guda 105 a fadin kasar Sin, wadanda suka shafi dukkanin birane, larduna da yankuna masu cin gashin kansu na kasar.
Lamarin da ya nuna cewa, aikace-aikacen kasuwanci dake tsakanin kasa da kasa da kasar Sin ta yi sun farfado da tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa. Za su kuma farfado da harkokin sayayya a kasuwannin duniya, wadanda aka dakatar da su na gajeren lokaci sanadiyyar barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Manufofin raya tattalin arziki da gwamnatocin kasa da kasa suka gabatar ba za su amfana ba, idan ba a tafiyar da tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa yadda ya kamata ba. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China