Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika CDC ta yabawa tallafin da Sin ta baiwa Afrika don yaki da COVID-19 a Afrika
2020-04-21 10:10:37        cri
Mambobin tawagar jami'an lafiya na kasar Sin masu yaki da annobar cutar COVID-19 a ranar Alhamis sun isa Addis Ababa na kasar Habasha, inda suka gudanar da taron karawa juna sani a ranar Litinin tare da kwararrun jami'an cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika wato (Africa CDC).

Kwararriyar hukumar kiwon lafiya ta nahiyar ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yabawa kasar Sin saboda taimakon da take cigaba da bayarwa da kuma yin hadin gwiwa da Afrika wajen yaki da cutar COVID-19.

A taron musayar kwarewar da suka gudanar na rabin wuni a helkwatar AU, dukkan bangarorin biyu sun bayyana aniyarsu na karfafa hadin gwiwa da jajurcewa domin yaki da annobar.

Mambobin tawagar kwararrun kiwon lafiyar na kasar Sin sun gabatar da makala mai take "kalubaloli da matakan yaki da annobar COVID-19 a kasar Sin," sun buga misalai tare da amsa tambayoyin daga bangaren Africa CDC.

Jack Ma, wanda ya kirkiri babban kamfanin ciniki ta intanet na kasar Sin, ya sha alwashin bayar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya don yaki da annobar COVID-19 a karo na uku ga Afrika domin yakar annobar a nahiyar. Kayayyakin sun hada da kayan gwaje gwajen lafiya rabin miliyan da takunkumin rufe fuska sama da miliyan hudu.

Baya ga tura kwararrun masana kiwon lafiya na kasar Sin zuwa cibiyar Afrika CDC ta AU, da yin musayar kwarewa a tsakanin kwararrun, John Nkengasong, daraktan cibiyar Afrika CDC, ya ce akwai kuma wani shirin intanet da aka tsara inda jami'an yaki da cutuka na kasar Sin CDC da na Afrika CDC da sauran cibiyoyin kula da lafiyar al'umma dake nahiyar zasu dinga haduwa domin yin musayar kwarewa a lokaci bayan lokaci. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China