![]() |
|
2020-04-18 15:10:18 cri |
A game da sukan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa WHO kan cewa "ba ta dauki matakan da ya kamata ba, kuma ta boye yanayin yaduwar cutar", shugabannin kasashen Afirka sun bayyana ra'ayoyinsu.
Daga ranar 8 ga wata zuwa yanzu, shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat da shugaban kasar Afirka ta kudu da ke rike da ragamar jagorancin kungiyar a wannan karo, Cyril Ramaphosa da ma shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, da shugaban kasar Namibia Hage Geingob sun bayyana daya bayan daya a kafofin sada zumunta cewa, kungiyar tarayyar Afirka da ma kasashen Afirka za su bada cikakken goyon baya ga hukumar WHO da ma babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, sun kuma yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali wajen hada kansu domin yaki da cutar a maimakon dora laifin cutar a kan wasu.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China