Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta karfafa ayyukan gyaran tsofaffin unguwannin dake birane
2020-04-17 11:44:34        cri

Mahukuntan kasar Sin, sun sha alwashin gudanar da ayyukan gyara tsofaffin unguwannin al'ummu mazauna birane cikin shekarar nan ta 2020. Karkashin wannan manufa dai za a yiwa unguwanni 39,000 kwaskwarima, aikin da zai amfani iyalai da yawan su ka iya kaiwa miliyan 7.

A cewar mataimakin ministan ma'aikatar muhalli da raya birane da karkara na kasar Huang Yan, ayyukan da za a gudanar kafin karshen shekarar ta bana, za su shafi fannonin inganta kayayyakin more rayuwa, da muhalli, da kyautata hidmomin da al'umma ke bukata, kamar na kula da tsofaffi da yara kanana.

Huang Yan ya kara da cewa, za a gundanar da ayyukan kwaskwarimar ne cikin tsari da inganci, gwargwadon bukatun al'ummu mazauna unguwannin. Kaza lika za a lura sosai da ingancin aiki da kaucewa hadurra. A hannu guda kuma, za a shigar da al'ummun da ayyukan za su shafa cikin su, domin tabbatar da dorewar tsarin lura da unguwanni da ake da shi.

A bara dai mahukuntan kasar Sin sun gyara tsofaffin unguwannin kasar har 19,000, aikin da ya kyautata yanayin muhallin iyalai da yawan su ya kai miliyan 3.52. Kididdiga ta nuna cewa, a halin yanzu, an fara ci gaba da gudanar da ayyuka dadan daban bisa managarcin tsari yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China