![]() |
|
2020-04-17 11:40:05 cri |
To sai kuma wani masani a fannin na ganin cewa, fakewa da batun cutar COVID-19, don "kawar da Sin daga tsarin masana'antu na duniya", ba shi da wata ma'ana, illa dai kawai cimma buri na siyasa.
Babban manazarci dake ofishin nazarin tattalin arzikin kasa da kasa na Petersen dake Amurka Nicholas R. Lardy, ya yi hasashen cewa, ba zai yi yiwuwa ba a kaurar da masana'antun samar da kayayyaki daga kasar Sin zuwa sauran sassan kasa da kasa bisa babban mataki.
Ya ce, ya zuwa yanzu, matsayin da Sin take rike da shi a sha'anin samar da kayayyaki a duniya, na da alaka sosai da nagartaccen tsarinta da ya bunkasa cikin gomman shekaru, da kuma ingantattun manyan ababen more rayuwa da take da su, har ma da masana, da kwadago masu kwarewa, da dai sauran gaggarumin rinjaye da take da su a wannan fanni, idan an kwatanta da sauran kasashe, kuma matsayi ne da manyan kamfanonin kasa da kasa suke ba ta bayan yin takara.
Ya ce, shekaru da dama da suka gabata, Sin ta rika samar da kayayyaki masu dimbin yawa, don biya bukatun gida da na waje bisa rinjayen da take da shi, wato cikakken tsarin samar da kayayyaki dake samar da kayayyaki marasa tsada kuma masu inganci. Manyan kamfanonin kasa da kasa su da kansu su tsai da kudurin zuba jari a kasar Sin.
Wasu Amurkawa na yin kira ga kamfanonin samar da kayayyaki dake kasar Sin da su koma Amurka, amma fa hakan ya danganta da masu sayayya na Amurka, wato ga misali ko suna son sayen wayar I-phone a farashin dala fiye da dubu 2, ko sayen safar kafa kan kudi har dala 25?
Jaridar "Financial Times" ta Birtaniya ta ba da wani bayani dake cewa, COVID-19 wata cuta ce dake dabaibaye dukkanin fadin duniya, amma ba wani rikici ne ga tsarin bunkasa duk duniya gaba daya ba. Don haka hanya daya tilo da za a bi wajen tinkarar wannan mumunar cuta, da kuma raya tattalin arziki, ba shakka ita ce ta hadin kai. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China