Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Sake bude Wuhan" ya kara imani da karfi kan tattalin arzikin kasar Sin
2020-04-16 21:06:35        cri

Me ya sa kasar Sin take cike da imani kan cimma burinta kan ci gaban tattalin arziki da al'umma? Birnin Wuhan da aka sake budewa a kwanaki 8 da suka gabata ya ba mu amsa.

A matsayinsa na birni mai muhimmanci a fannin tattalin arziki dake yankin tsakiyar kasar Sin, a shekarar 2019, birnin ya kai matsayi na 8 a jerin sunayen birane a fannin GDP, kana wuri da ya shahara a fannin kera motoci a kasar ta Sin, wannan ya sa aka kafa sansani mafi girma na kamfanonin sadarwa a kasar Sin har ma a duniya baki daya, hakan yana da muhimmanci kwarai wajen tabbatar da tsarin sana'o'in da suka shafi motoci da sadarwa ta hanyar kamputa da dai sauransu har ma da tsarin sana'o'i na daukacin duniya. Sake bude birnin Wuhan zai taimaka wajen farfado da tsarin sufurin kasar Sin da komawa bakin aiki a duniya.

A matsayinsa na kafa mai muhimmanci ga inganta ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a cikin shekaru 6 da suka gabata a jere, yadda ake sayen kayayyaki na da nasaba sosai da yanayin tattalin arzikin kasar. Yaya za a kawar da tasirin da yanayin annobar ke haifarwa kamfanoni daban daban, wannan ita ce muhimmiyar hanyar raya tattalin arzikin kasar. Tun daga ranar 30 ga watan Maris, dukkan fannonin da suka shafi kasuwanci a birnin Wuhan sun soma komawa bakin aiki daya bayan daya. A waje guda kuma, an kaddamar da jerin matakai a wurin don rage haraji da nuna goyon baya a fannin kudi da dai sauransu don taimakawa ci gaban kanana da matsakaitan kamfanoni.

Kamar yadda Wuhan ya yi, kamfanonin dake wurare daban daban na kasar Sin su ma suna tinkarar wahalhalu ta hanyar kare kansu ko kuma samun tallafi daga waje.

Birnin Wuhan da ya ci jarrabawar annobar, a yanzu haka ya soma farfado da tattalin arzikinsa, kana ya nuna nauyin dake wuyansa na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga duk bil Adama. Kasar Sin dake hadin kan al'umma da kara kokari, kana kasar da ke da kwarewa wajen tinkarar matsala, ba kawai tana da imani da karfi wajen cimma burinta na samun ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma a bana ba, har ma za ta ci gaba da kara imani da karfin tattalin arzikin duniya baki daya.(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China