Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tura tallafin kiwon lafiya kashi na 2 Algeria don yakar COVID-19
2020-04-16 09:17:14        cri

A ranar Laraba kasar Algeria ta karbi kashi na biyu na tallafin kayayyakin kiwon lafiya daga kasar Sin, domin taimakawa kasar ta arewacin Afrika yaki da annobar COVID-19.

Jirgin saman da aka loda kayan tallafin kiwon lafiyar ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa dake Algiers wanda ya samu tarbar mataimakin ministan masana'antun hada magunguna na kasar Lotfi Djamel Benbahmed da jakadan Sin dake Algeria Li Lianhe.

Benbahmed ya fadawa manema labarai cewa, kayayyakin kiwon lafiyar sun hada da takunkumin rufe fuska, kayayyakin gwaje gwaje, da rigunan baiwa jami'an lafiya kariya.

Ya ce tallafin kayayyakin ya kara bayyana yadda girman dadaddiyar dangantaka a tsakanin Algeria da Sin.

A nasa bangaren, jakada Li ya ce, Algeria da Sin suna da kyakkyawar dangantaka mai karfi a tsakaninsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China