Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasan Tai Chi da wasan Tai Chi tare da mafifici
2020-04-16 14:29:56        cri

Ban da wasan Tai Chi, akwai wani sabon wasan da aka haifar da daga wasan Tai Chi, shi ne wasan Tai Chi tare da mafifici. Wato wanda ake rike wani mafifici da yin wasan Taichi. Wang Xing, malama ce da ta ke koyar da fasahohin wasan Tai Chi tare da mafifici a kasar Sin. Ta fara koyon wasan Tai Chi tun daga lokacin kuruciyarta, ta koyi wasan daga wajen mahaifinta a garinta dake ta Chenjiagou dake lardin Henan na kasar Sin, wato wurin da aka fara yin wasan Tai Chi na kasar Sin.

Ya zuwa yanzu, ta riga ta koyi wasan Tai Chi har na tsawon shikaru fiye da 20. Ta ce, wasan Tai Chi shi ne tushen wasan Tai Chi tare da mafifici, ya kamata wanda ya iya yin wasan Tai Chi, ya yi amfani da mafifici tare da yin wasan Tai Chi tare. Babu shakka, wannan wasa na iya taimakawa mutane wajen motsa jiki, da kiwon lafiyar jiki. Haka kuma, daukar mafifici ya fi sauki ga mutane, fiye da buga wannan wasa mai kyaun gani kuma mai ban sha'awa.

A hakika dai, an kirkiro wannan wasa ne a shekarar 2008, wato shekara ce ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, inda wasu masu sha'awar wasan Kongfu na kasar Sin suka kirkiro wasan Tai Chi tare da mafifici, kana mutane dubu 10 sun yi wasan tare a gun bikin gasar. Don haka, wasan ya fara samun karbuwa a kasar Sin. Amma mafifici kayan gargajiya ne a kasar Sin, a lokacin da a kan yi amfani da shi a wurin yake-yake, da kuma zaman yau da kullum. A sakamakon hakan, Sinawa sun iya karbar wannan wasa.

Malama Wang ta ce, yin wasan Tai Chi tare da mafifici yana iya taimakawa mutane wajen kara karfin jikinsu, da kwantar da hankalinsu. Ta ce,

"Wasan yana taimakawa kiwon lafiyar jikin mutane, da kuma yanayin zuciyarsu. Yayin da ake yin wasan, ya kamata a yi amfani da mafifici kwarai, da kara karfin jikin mutane don daukar mafifici da yin wasan Tai Chi tare. Kana mafifici yana da kyaun gani, yayin da mutane ke yin wasan, za su kwantar da hankalinsu da jin dadin wasan."

Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 a halin yanzu, ba a iya fita waje, ba a iya yin wasannin motsa jiki a waje, don haka wannan wasa ya zama wata hanya mai dacewa wajen kiyaye lafiyar jikin jama'a. Domin babu bukatar samun wuri mai fadi wajen buga shi, kana ana iya yin shi a kowace rana. Malama Wang ta gaya mana cewa,

"Yayin da muke yin wasan Tai Chi tare da mafifici, hankalinmu zai kwanta, za a inganta karfinmu na zuciya da numfashi, musamman kara karfin huhunmu. Cutar COVID-19 cuta ce da take kawo illa ga huhu da numfashi, don haka idan mu kara karfin numfashi da huhunmu a halin yanzu, za mu iya kara karfin tinkarar cutar COVID-19."(Zainab)


1  2  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China