Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mujallar Focus: Akwai dalilai guda 4 da ake zuba jari a kasar Sin
2020-04-14 20:42:22        cri
Mujallar Focus ta kasar Jamus da ake bugawa mako-mako a jiya Litinin ta wallafa wani sharhi mai taken "Dalilai guda hudu da ake sayen hannayen jari na Sin, inda aka nuna cewa, yanzu kusan ba a samu sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ba, sai sabbin wadanda ke shigo da cutar daga ketare, kuma da alamun tattalin arzikin kasar yana farfadowa cikin sauri fiye da yadda aka yi hasashe. Haka kuma masana'antu da masu zuba jari suna cike da imani kan tattalin arzikin kasar. Akwai dalilai guda hudu na zuba jari a kasar Sin yanzu.

Da farko, kasar Sin ne take kan gaba a duniya baki daya. A yayin da ake samun yaduwar cutar a Turai da Amurka, nasarar da Sin ta cimma ta dalike cutar ta kawo fata ga duk duniya na warware matsalar. Wannan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai sake bunkasa cikin sauri.

Na biyu, ya zuwa yanzu, shaidu sun cewa, kasuwar hannayen jarin kasar Sin ta fi ta Turai da Amurka karfin tinkarar hadari.

Na uku, masu zuba jari na farin ciki. Kwanan nan, wasu manyan masu zuba jari na kasa da kasa sun sayi hannayen jari na kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin Tencent. A takaice dai, manyan masu zuba jari za su sake nuna sha'awarsu kan kamfanonin kasar Sin cikin sauri.

Na hudu, bukatun cikin gida ya karu. Kasar Sin a yanzu haka ta sha banban da yadda take a 'yan shekarun da suka gabata. Yawan masu matsakaicin karfi na karuwa, kuma matsayin sayen kayayyaki na al'ummar kasar shi ma na karuwa. A don haka, nan gaba, wannan babbar kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya mai yawan al'umma biliyan 1.4 na cike da damammaki. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China