Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya jaddada bukatar hada kai don ganin bayan COVID-19 a gabashin Asiya
2020-04-14 20:13:31        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar kara fadakar da al'umma kan makomar bai daya ga daukacin bil-Adama, ta yadda za a yi nasarar ganin bayan cutar COVID-19 a yankin gabashin Asiya.

Li ya bayyna haka ne Talatar nan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, yayin da ya halarci taron kolin musamman na kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya da Sin da Japan da Koriya ta kudu ta kafar bidiyo kan cutar COVID-19.

Ya kuma yi kira ga kasashen, da su nuna halaye na gari da rawa na musamman da za su taka wajen yaki da cutar da farfado da tattalin arziki, kana su aiko da sakon hadin gwiwa da taimakon juna tsakanin kasashen yankin gabashin Asiya, don kara imanin yankin da ma sauran kasashen duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China