Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya gabatar da jawabi game da yakin da kasarsa ke yi da cutar COVID-19
2020-04-14 12:57:27        cri

Da almurun jiya Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da jawabi na musamman ga 'yan kasa, don gane da yanayin da Najeriyar ke ciki game da yaki da cutar numfashi ta Covid-19.

Cikin jawabin na sa, shugaban ya yi waiwaye game da umarnin zama a gida na mako 2 a jihohin Lagos da Ogun, da birnin tarayyar kasar Abuja, wanda ya shelanta cikin jawabin sa na ranar 29 ga watan Maris da ya gabata, inda ya ce hakan ya sa wasu karin jihohin kasar rungumar wannan mataki.

Shugaba Buhari ya ce, a matsayin su na zababbu, kuma jagororin al'umma, sun zabi aiwatar da matakai masu tsauri, duk kuwa da sanin halin matsi da hakan zai haifar ga al'umma baki daya. Sai dai duk da haka, a cewar shugaban, hakan sadaukarwa ce da daukacin 'yan Najeriya za su yi domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar. Ya ce mataki ne na kare rayuwar al'umma baki daya. Kana hakan zai ba da damar lokaci, da filin aiki cikin gaggawa, ga jami'an da ke sahun gaba wajen yaki da wannan annoba.

Ya ce ko shakka babu, 'yan Najeriya sun rungumi wannan manufa ta zama a gida a kusan dukkanin sassan kasar. Don haka ya mika godiya ga 'yan kasar, bisa sadaukarwa da suke ci gaba da yi musamman a wannan muhimmin lokaci.

Shugaba Buhari ya ce, bisa dumbin goyon baya da hadin kan dukkanin sassa, Najeriya ta cimma manyan nasarori a yayin wannan lokaci na zama a gida.

Daga nan sai ya bayyana fatan cewa, ko shakka babu, ta hanyar ci gaba da aiki tukuru, Najeriya za ta cimma nasarar kawo karshen wannan cuta cikin nasara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China