Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu dabaru uku da Amurka take amfini da su domin bata sunan kasar Sin
2020-04-12 19:32:32        cri

Yakar cutar numfashi ta COVID-19 na bukatar a hada kan duniya baki daya, amma wasu 'yan siyasar kasar Amurka suna amfini da wannan yanayin annobar don shafawa kasar Sin kashin kaji, da kuma kare kansu a fannin siyasa. Siyasantar da batun cutar, dorawa saura laifi, da kuma kyautata siffarta, sun kasance wasu dabaru uku da kasar Amurka take amfani da su domin samun moriya a yayın da ake dalike cutar. Wasu kafofin watsa labarun kasar kuma suna ta kara musu kwarin gwiwa a fannin.

Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ba ya la'akari da gargadin da masana suka yi masa, da kyale tasirin da cutar ke kawowa, har ma ya ce wai dora muhimmanci sosai kan cutar wasan yaudara ne na jam'iyyar demokuradiyya.

Bisa tabarbarewar yanayin annobar, gwamnatin Trump na yunkurin boye kuskuren da ta yi a yayin yakar cutar. Ko da yake, har yanzu masana suna kokarın binciken asalin cutar, amma Trump da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo suna ta yin amfani da nada sunan cutar don bata sunan kasar Sin.

Bisa yaduwar cutar a duk duniya kuma, kasar Amurka ta soma mayar da kanta a matsayin kasa mai nuna jin kai mafi girma a duniya, wadda kuma ba a taba ganin irinta ba a tarihi.

Gaskiya wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labarun kasar sun yi yunkurin gayawa duniya wani labari na daban ne game da cutar. Amma, a yayin da ake tinkarar wannan cutar mai tsanani, kamata ya yi kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, kuma bisa hakikanin halin da ake ciki.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China