Africa CDC: Adadin mutanen da COVID-19 ta halaka a Afrika ya kai 700 mutane 13,145 sun kamu da cutar
2020-04-12 17:21:53 cri
Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Afrika wato Africa CDC ta sanar cewa, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a Afrika ya zarce 700 yayin da mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 13,145 a duk fadin nahiyar ya zuwa ranar Asabar.
Hukumar dake yaki da bazuwar cutuka a nahiyar ta kara da cewa, mutane 2,171 sun warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar Afrika.