![]() |
|
2020-04-12 17:16:28 cri |
Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar yace, ya zama tilas a bukaci al'ummar kasar dasu kara takaita zirga zirga a duk inda suke a fadin kasar domin mutunta shawarwarin kwararrun masana kiwon lafiya.
Sanarwar tace, mutanen da suka fi fama da matsin rayuwa a kasar, gwamnati ta sanar da daukar matakai daban daban domin tallafa musu, daga ciki akwai fitar da ton 70,000 na hatsi da gwamnatin tarayya ta adana a rumbunan ajiyarta domin rabawa ga mutane masu tsananin bukata, da kuma bada tallafin kudade ga masu karamin karfi, kuma gwamnatin tarayyar kasar, da jihohi da kuma kananan hukumomi zasu cigaba da bayar da tallafin ga jama'a.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China