Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Ya kamata dukkan kasashe su guji mayar da COVID-19 siyasa
2020-04-12 17:06:19        cri
Cui Tiankai, jakadan kasar Sin a Amurka yace kamata yayi dukkan kasashen duniya su mayar da hankali wajen bada gudunmowa ga kasa da kasa game da ayyukan dakile annobar COVID-19, a bada fifiko ga rayuka da lafiyar al'umma kuma a yi watsi da duk wani yunkurin siyasantar da batun annobar.

Jakada Cui ya bayyana hakan ne a yayin hira da ya yi ranar 3 ga watan Afrilu da Ian Bremmer a shirin Gzero World, wacce tashar talabijin ta Amurka ta watsa a ranar Asabar.

Ya ce wannan babbar matsala ce da ta shafi kowa da kowa, jakadan yayi watsi da zarge zargen da wasu 'yan siyasar yammacin duniya ke yi cewa kasar Sin tana da wata manufar siyasa wajen tallafawa sauran kasashen duniya don yaki da annobar.

A cewarsa babban abin da muke taimakawa sauran kasashe shi ne sabo da dukkan al'ummar duniya makomarsu daya ce. Yace kasar Sin ba zata taba zama cikin kwanciyar hankali ba idan dukkan kasashen duniya suna fama da yaki da annobar, asali ma muna taimakon kanmu ne ta hanyar taimakawa sauran kasashe, in ji jakadan na Sin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China