Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hasashen IMF ya nuna za a samu koma bayan kudin shiga a sama da kasashe 170 a bana
2020-04-10 10:59:30        cri
Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta ce hasashen asusun ya nuna cewa, sama da kasashe 170 za su fuskanci koma bayan kudin shigar kowanne dan kasa a bana.

A jawabin da ta yi jiya, gabanin taron lokacin bazara da za a yi a mako mai zuwa, ta ce kasashen duniya na fama da annobar da ba a taba gani ba.

Ta ce cutar COVID-19 ta yi saurin kawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa a wani yanayi da ba a taba gani ba a tarihi.

Shugabar asusun na IMF, ta ce a bayyane yake cewa, tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma baya a bana, tana mai cewa ana sa ran ganin tabarbarewar tattalin arziki mafi muni.

Domin tunkarar annobar, Kristalina Georgieva, ta gabatar da wasu shirye-shirye 4 da suka hada da; ci gaba da daukar matakan dakile cutar da tallafawa tsarukan lafiya, sai kare mutanen da suka kamu da kare kamfanoni bisa daukar wasu matakai a bangaren hada-hadar kudi, sai rage matsi kan tsarukan hada-hadar kudi; sai kuma shiryawa lokacin da za a farfado da rage tasirin annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China