![]() |
|
2020-04-08 10:52:01 cri |
Baki daya jimillar mutane 72,776 ne suka mutu a fadin duniya a sanadiyyar annobar COVID-19, yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ya kai 1,282,931 ya zuwa ranar Talata, kamar yadda alkaluma na baya bayan nan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar.
A cewar WHO, ya zuwa karfe 10 na daren Talata, nahiyar Turai tana da jimillar mutane 686,338 da suka kamu da COVID-19, yayin da rahotanni suka bayyana cewa, Amurkawa 384,242 ne aka tabbatar sun harbu da cutar ta COVID-19.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China