Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WAHO ta sha alwashin hana yankewar kayan kula da lafiya ga kasashen yammacin Afirka
2020-04-03 13:25:48        cri
Hukumar lafiya ta yammacin Afirka ko WAHO a takaice, ta ce ba bukatar nuna damuwa game da yiwuwar yankewar kayan kula da lafiya a yankin, a gabar da yanzu haka ake ci gaba da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Cikin wata sanarwa wadda ofishin WAHOn ya fitar a ranar Alhamis, ya ce hukumar na aiki kafada da kafada da sauran abokan hulda na sassan duniya daban daban, don tabbatar da cewa, kayayyakin da ake bukata domin kiwon lafiya ba su yanke a kasashen yankin ba.

Tuni dai hukumar ta raba kayan gwajin kwayar cutar COVID-19 har 30,000 ga kasashe mambobin hukumar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China