2020-03-31 20:58:43 cri |
Madam Hua ta ce, kullum kasar Sin tana gudanar da harkokinta ne ba tare da wata rufa-rufa ba, da ma sanar da hukumar lafiya da duniya (WHO) da kasashen duniya kan abin da take yi, ciki har da raba yanayin halittar kwayar cutar a kan lokaci tun lokacin da wannan annoba ta barke.
Haka kuma kasar Sin, tana shiga hadin gwiwar kasa da kasa don yaki da wannan annoba, sannan kasarta ta taimakawa bangarori daban-daban tare da samar da taimako ga wasu kasashe.
A baya-bayan nan ne dai, Navarro ya zargi kasar Sin yayin wata hira, inda ya ce wai ta mayar da kasashen duniya baya na tsawon makonni shida, saboda rashin fadawa sauran kasashe cewa, wani yana iya yada cutar COVID-19 ga wani, zargin da mahukuntan kasar ta Sin suka yi Allah wadai da shi.
Madam Hua ta ce mece ce manufar dan siyasar ta Amurka? Abin da ya ke nema shi ne jirkita gaskiya, ya kuma dorawa wasu laifi, da lalata alakar Sin da Amurka kan yaki da wannan annoba, da ma hadin gwiwar kasashen duniya a wannan fanni.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China