Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kokarin samar da hidimar amsa tambayoyi kan lafiyar jiki ta Intanet domin taimaka wa duniya wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-26 13:23:37        cri

A kokarin da ake na taimaka wa jama'a fahimtar cutar COVID-19 da kara kare kansu daga cutar, wasu kamfanonin raya harkoki ta intantet na kasar Sin sun himmatu wajen samar da hidimar amsa tambayoyi kan lafiyar jiki ta Intanet, a kokarin taimakawa duniya yaki da wannan cuta.

"Yanzu haka na killace kaina a gidana a birnin Milan da ke kasar Italiya. Kullum ina tuntubar likitoci ta manhajar Alipay, kuma bisa shawarwarin da suke bayarwa, yanzu hankalina ya kwanta. Ina fatan za a hanzarta kawo karshen cutar. Ta yadda zan koma gidana."

Masu sauraro, kalaman wani Basine da ke kasar Italiya kuka saurara. Hakika, tun bayan bullar cutar COVID-19, Sinawan da dama da ke kasashen waje na ganin likita ta manhajojin yanar gizo dake samar da hidimomin lafiya, a kokarin kara kare kansu daga cutar. A cikin watanni biyu da suka gabata, Wang Qiaomu, wata likita dake aiki a asibitin Jami'ar Donghua da ke birnin Shanghai na samar da hidimar amsa tambayoyi kan lafiyar jiki, ciki kar da cutar COVID-19 ta manhajar yanar gizo ta Alihealth kyauta. Kuma ta bayyana cewa, a 'yan kwanakin nan, karin Sinawan da ke zaune a ketare na yi mata tambayoyi.

"Wasu sun tambaye ni cewa, yanzu ina tari, shin na kamu da cutar COVID-19 ke nan? Yanzu zafin jikina ya kai digiri 36.7, shin akwai zazzabi ko a'a a jikina? Ban samu marufin hanci da baki da likitoci suka amince ba yanzu, idan na yi amfani da marufin hanci da baki guda biyu zai taimaka? Ta yaya za a yi rigakafin cutar COVID-19? Wadannan su ne tambayoyin da muke yi a lokacin bullar cutar a kasarmu."

Ban da wannan Wang Qiaomu ta furta cewa, a kwanakin nan, ta kan amsa tambayoyin daga Koriya da Kudu, Malaysia da sauran kasashen Asiya da rana, sa'an nan kuma bayan karfe 10 na dare, ta kan amsa tambayoyin daga kasashen Amurka, Birtaniya da Italiya da dai sauransu. Yawan mutanen da ke neman shawara daga wajenta ya kai kimanin 15 a cikin awa guda.

"A wani bangare, muna so mu taimaka musu wajen samun bayanai game da matakan kariya daga cutar. Kamar yadda ya kamata a sanya marufin hanci da baki? Gaskiya, ba su sani ba. Ba su san yadda za a bambanta ciki da wajen marufin hanci da baki ba. Hakika dai, a farkon yaki da cutar, mu al'ummar Sin ba mu san wannan ba. Matsalolin da wurare daban daban na duniya ke fuskanta duk daya ne. Ban da wannan kuma, suna jin tsoron cutar sosai. Fargaba da suke yi kan yadda cutar za ta haddasa rashin lafiyar jiki, ya sa muke so mu taimaka musu wajen rage wannan fargaba."

Rahotanni na cewa, a cikin watanni biyu da suka gabata, akwai likitoci fiye da 700 dake dukufa wajen samar da hidimar amsa tambayoyin lafiya kamar yadda Wang Qiaomu ke yi. A ciki, likitoci kusan dari daya sun shiga aikin ceton wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a lardin Hubei na kasar Sin, inda cutar ta fi kamari.

Wannan manhajar yanar gizo da wadannan likitoci ke amfani da ita, mahaja ce da Asusun jin dadin jama'a na Jack Ma da Asusun jin dadin jama'a na Alibaba suka tsara tare. Kuma ya zuwa ranar 23 ga wata, Sinawan da ke ketare fiye da dubu dari sun shiga manhajar don neman shawarwarin likitoci.

A kwanan nan kuma, wani kamfanin cinikayya ta Intanet na kasar Sin wato Kamfanin Jingdong shi ma ya sanar da samar da hidimar amsa tambayoyin lafiyar jiki kyauta, ya kuma kunshi likitoci daga dukkan fannoni, ciki har da fannin cuttuttuka masu yaduwa da ilmin numfashi. An kuma tattara masana ilmin likitancin gargajiya fiye da 30 domin ba da taimako wajen yaki da cutar bisa ilmin likitancin gargajiyar Sin. Haka zalika, akwai likitoci fiye da 20 dake iya amsa irin wadannan tambayoyin da harshen Turanci.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China