Firaministan kasar Japan Shinzo Abe, da shugaban kwamitin kasa da kasa na shirya gasar Olympic Thomas Bach, sun amince da dage gasar wasannin Olympic na birnin Tokyo zuwa a kalla lokacin zafi na shekarar 2021 mai zuwa, kamar dai yadda sanarwar fadar firaministan Japan din ta sanar.