Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Trump ya lura da harkokin kasarsa da kyau maimakon bata sunan sauran kasashe
2020-03-24 20:39:12        cri

 

Jaridar New York Times ta wallafa wani sharhi dake cewa, babban dalilin da ya sa Donald Trump ya kira "kwayar cutar COVID-19" da sunan "kwayar cutar China" shi ne, domin karkata hankalin al'umma, a wani yunkuri na wanke kansa daga babban kayen da ya sha, a fannin tinkarar annobar cutar a Amurka.

Kana kuma, tashar intanet ta The Daily Beast ta Amurka ta ruwaito cewa, fadar White House na kokarin hada kan hukumomi da dama, don su cimma matsaya kan dorawa kasar Sin alhakin barkewar cutar COVID-19 a Amurka, da ma a duk fadin duniya baki daya.

 

 

Dora laifi kan kasar Sin, wayo ne da gwamnatin Trump ta dade tana amfani da shi wajen bata sunan Sin. Yayin da cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duniya, kamata ya yi Trump ya lura da harkokin kasarsa da kyau, ya maida hankalinsa kan daukar managartan matakan kandagarkin yaduwar cutar, ciki har da nazarin adadin mutanen da suka kamu da cutar, da baiwa masu fama da cutar magani yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China