Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kallace da kuma binciki lafiyar duk wanda ya shigo birnin Beijing daga ketare
2020-03-24 14:03:54        cri

A halin yanzu, ana samun yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri a wasu kasashen waje, hakan ya kara kawo barazanar shigo da cutar daga mutanen da ke zuwa kasar Sin. Tun daga ranar 25 ga wannan wata, za a dauki sabon matakin magance yaduwar cutar a birnin Beijing, inda za a bukaci yin binciken lafiyar dukkan mutanen da suka shigo kasar Sin ta birnin Beijing daga ketare, tare da killace su.

Kafin wannan, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin ta ce tun daga ranar 23 ga wata, dukkan jiragen saman da suka tashi daga kasashen waje zuwa birnin Beijing na kasar Sin sun sauka a sauran filayen jiragen sama 12 na kasar Sin, ciki har da Tianjin, da Shijiazhuang, da Taiyuan da sauransu.

Filin jiragen sama na kasa da kasa na Beijing, muhimmin filin jiragen saman kasa da kasa ne a kasar Sin, inda ake zirga-zirgar jiragen sama kimanin 200 a kowane mako a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya 33 kamar su Amurka, da Koriya ta Kudu, da Faransa da sauransu, don haka ana kara fuskantar kalubalen shigar da mutanen dake dauke da cutar daga sauran kasashe zuwa kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China