![]() |
|
2020-03-23 13:06:31 cri |
A ranar 19 ga watan nan, Zhong Nanshan, Madam Li Lanjuan, da wasu kwararrun kasar Sin da suka shahara a duniya sun yi karin bayani filla-filla ga takwarorinsu na kasashen ketare kan fasahohin kasar Sin wajen yaki da cutar ta COVID-19 a yayin taron musayar fasahohin yaki da cutar na duniya, wanda aka gudanar ta kafar Internet.
Daya daga cikin hanyoyin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen dakile yaduwar cutar cikin hanzari shi ne, gaggauta yanke shawara kan ko wani ya kamu da cutar ko a'a, da ba shi magani bisa yanayin lafiyarsa. A cikin takardar jagora kan kandagarki da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da aka sake wallafawa karo na 7, kasar Sin ta yi cikakken bayani kan yadda take yaki da annobar ba tare da rufa-rufa ba.
Kwanan baya, shugabannin wasu kasashe, ciki har da na kasar Czech, sun nuna wa kasar Sin godiya tare da fatan koyon fasahohin Sin don hana yaduwar annobar a kasashensu. Sa'an nan kuma, masu amfani da Internet a sassa daban daban na duniya sun jinjina wa likitocin kasar Sin, tare da bayyana su a matsayin jarumai na hakika. (Tasallah Yuan daga CRI)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China