2020-03-23 11:14:33 cri |
A jiya 22 ga wata, an kaddamar da tsarin da masu ba da hidimar lafiya za su rika tattaunawa da marasa lafiya ta kafar bidiyo a asibitin Kenyatta dake birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. An yi amfani da fasahar daukar hoton bidiyo daga nesa da kasar Sin ta samar a cikin wannan tsarin dake iya taimakawa kasashen Afirka wajen dakile cutar numfashi ta COVID-19. A yayin kaddamar da tsarin, likitocin kasar Kenya sun yi hira tare da takwarorinsu dake birnin Beijing da na Wuhan na kasar Sin ta kafar bidiyo, inda suka more fasahohin dakile cutar da kasar Sin ta samu.
Babban kamfanin Neusoft na kasar Sin ne ya samar wa asibitin Kenyatta wannan tsari, inda ya kunshi na'urorin tantance cutar numfashi ta COVID-19, da na daukar hoton bidiyo da kuma na'urorin daukar hoton sassan jiki wato CT wadanda za su iya taimakawa likitocin asibitin wajen bincike da kuma tantance wadanda suka harbu da cutar. Mr. Mutahi Kagwe, ministan lafiyar kasar Kenya ya bayyana cewa, wannan tsarin yana da muhimmanci sosai ga kasar Kenya. Ta hanyar yin hira da kuma tattaunawa kan cutar da likitocin kasar Sin, za a iya taimakawa kasar Kenya wajen yin rigakafi da kuma dakile cutar COVID-19, sannan za a iya rage illar da cutar za ta haifarwa kasar Kenya. Mr. Mutahi Kagwe yana fatan kasarsa za ta iya hada kan sauran kasashen duniya kan yadda za su iya kara yin musayar fasahohi da hidimomin dakile cutar, ta yadda ba kawai za a iya kawo wa 'yan Kenya fatan alheri ba, har ma ga dukkan daukacin bil Adama. Mr. Mutahi Kagwe yana kuma nuna wa kasar Sin godiya sosai.
"Bisa wannan fasaha, za mu iya gayyatar likitocin sauran kasashen duniya tamkar suna gabanmu maimakon jigilar marasa lafiyar mu zuwa ketare. Wannan sakamako ne da fasaha ta kawo mana. Ina son nuna godiya matuka ga gwamnati da kungiyoyin kasuwanci na kasar Sin da fasahohin zamani da suka samu."
Kawo yanzu, yawan mutanen kasar Kenya wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 ya kai 15, kuma galibinsu yanzu suna samun jinya a asibitin Kenyatta dake birnin Nairobi. A yayin bikin kaddamar da wannan tsarin da masu ba da hidimar lafiya za su rika tattaunawa da marasa lafiya ta kafar bidiyo, ma'aikata masu aikin jinya na asibitin Kenyatta sun tattauna kan yanayin da wadannan mutane da suka harbu da cutar suke ciki da farfesa Jin Zhengyu da tawagarsa daga asibitin Peking Union Medical College da wasu kwararrun likitoci wadanda suka fito daga birnin Wuhan na kasar Sin, inda masanan kasar Sin suka taimakawa takwarorinsu na Kenya kan yadda za su iya mallakar fasahohin dakile cutar cikin sauri.
Dr. Nicholas Gumbo, shugaban asibitin Kenyatta ya bayyana cewa, tsarin da masu ba da hidimar lafiya za su rika tattaunawa da marasa lafiya ta kafar bidiyo ya ba da taimakon fasaha wajen tantance wadanda suka harbu da cutar da wuri. Dr. Nicholas Gumbo yana mai cewa, "Za mu yi amfani da bayanan kwamfuta da fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI) wajen tantance wadanda suka harbu da cutar, fasaha tana da muhimmanci matuka ga kokarin shawo kan cutar numfashi ta COVID-19. Bisa irin wadannan tsare-tsare, mun yi musayar fasahohin dakile cutar da masanan Beijing da Wuhan na kasar Sin kai tsaye, sannan mun hade wannan tsarin da irin wadannan tsare-tsaren da ake da su a jihohi 37 na kasar Kenya. Wannan shi ne tsarin farko da masu ba da hidimar lafiya za su rika tattaunawa da marasa lafiya ta kafar bidiyo a duk fadin Afirka."
Rahotanni na cewa, yanzu haka an riga an samar wa jihohi 37 na kasar Kenya injunan daukar hotunan marasa lafiya na zamani da fasahar more irin wadannan hotuna da kuma hidimar samar da hoto a asibiti, har ma da shirin dakile cutar gaba daya. Yawan mutanen da wannan tsari zai shafa zai kai kashi 70 cikin dari na daukacin al'ummar kasar Kenya. (Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China