Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka ta Kudu ta sanar da daukar kwararan matakai domin tinkarar annobar COVID-19
2020-03-16 13:29:20        cri

Da daren jiya Lahadi, shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya sanar da ayyana annobar cutar numfashi ta COVID-19 dake bazuwa a kasar a matsayin "iftila'in kasa", kana gwamnatinsa za ta dauki kwararan matakai da dama don shawo kan annobar.

Cyril Ramaphosa ya kira taron majalisar ministocin kasar cikin gaggawa, domin tattaunawa kan yadda za'a tinkari annobor cutar COVID-19. Bayan kammala taron, Ramaphosa ya fadawa kafofin watsa labarai cewa, gwamnatinsa ta yanke shawarar daga matsayin annobar zuwa "iftila'in kasa baki daya" da kara daukar kwararan matakai domin kandagarkin annobar. Cyril Ramaphosa ya ce:

"Bisa dokar shawo kan bala'u ta Afirka ta Kudu, yanzu ina sanar da ayyana annobar cutar COVID-19 a matsayin 'bala'in kasa'. Wannan zai taimaka mana wajen kafa cikakken tsarin shawo kan bala'u, da hana yaduwar annoba, da rage illar da take haifarwa. Haka kuma wannan zai taimaka mana wajen kafa ingantaccen tsarin tinkarar bala'u cikin gaggawa."

Ramaphosa ya kara da cewa, gwamnatin Afirka ta Kudu, ta yanke shawarar daukar wasu kwararan matakai, domin rage illar da cutar COVID-19 ke haifarwa ga kasar, ciki har da haramta yin tafiye-tafiye, inda ya ce:

"Mun yanke shawarar hana matafiya su shigo kasarmu daga wasu kasashe da cutar ta fi kamari, tun daga ranar 18 ga wata, ciki har da Italiya, da Iran, da Koriya ta Kudu, da Sifaniya, da Jamus, da Amurka, da Birtaniya, da kuma kasar Sin. Kuma mun hana jama'ar Afirka ta Kudu su tafi wadannan kasashe, ko kuma ratsawa ta kasashen. Har wa yau, an hana baki da suka taba zuwa kasashen da cutar COVID-19 ta fi kamari a cikin kwanaki 20 da suka gabata su shigo Afirka ta Kudu."

Sauran wasu matakan da gwamnatin Afirka ta Kudu ta dauka domin tinkarar cutar COVID-19 sun hada da, hana jami'an gwamnatin kasar su yi tafiya kasashen waje, da haramta shirya gangamin jama'a na fiye da mutane 100, da soke bukukuwan jama'a, da kuma dakatar da karatun makarantu daga ranar 18 ga wata, har zuwa tsakiyar watan Afrilu.

Cyril Ramaphosa ya jaddada cewa, yanzu illar da annobar cutar COVID-19 ke yi ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu a bayyane take, inda ya ce:

"Mu'amalar tattalin arziki tsakanin Afirka ta Kudu da wasu muhimman aminan cinikayyarta ta ragu sosai a makwannin da suka wuce. Sakamakon bullar cutar, gami da kwararan matakan da muka dauka, kuma yawan kayayyakin da muke fitarwa zuwa kasashen waje zai ci gaba da raguwa, kuma matafiyan da za su zo kasar mu don yawon bude ido za su ragu. Duk wadannan matsaloli za su yi mummunar illa ga harkokin kere-kerenmu, da kawo tsaiko ga ci gaban kamfanoni, har ma ga tattalin arzikin dukkan kasa baki daya."

Ramaphosa ya ce, gwamnatinsa za ta dauki managartan matakai domin tallafawa kamfanoni su haye wahalhalu, inda ya yi kira ga jama'ar kasar su natsu, da daina yada jita-jita ko labaran karya game da cutar. Ya ce, yana da yakinin Afirka ta Kudu, da sauran kasashen duniya za su samu galaba kan annobar cutar.

Cyril Ramaphosa ya ce:

"Muna da kwarewa da ilimi, muna da albarkatu da dabaru iri-iri domin yakar cutar COVID-19, haka kuma muna da aminai, sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da WHO, za su yi kokari tare da mu domin shawo kan cutar."

Kawo yanzu, an tabbatar da mutane 61 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Afirka ta Kudu, har ma a jiya Lahadi kacal, an samu karuwar mutane 23, abun da ya sa Afirka ta Kudu ta zama kasa da ta fi samun mutanen da suka kamu da cutar, a kasashen dake kudu da hamadar Sahara. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China