2020-03-12 14:28:56 cri |
Ban da mambobin kasashen kwamitin sulhun, wakilai na wasu kasashen Afirka, ciki har da Algeria, Angola, Djibouti, Habasha, Kenya da kuma Senegal da dai sauransu sun halarci muhawarar. Haka zalika, jami'ar sa ido ta kungiyar AU dake MDD Fatima Kyari Mohammed, da mataimakin babban sakataren Shirin raya kasashe na MDD (UNDP), kuma mashawarcin musamman na shugaban hukumar Abdoulaye Mar Dieye su ma sun halarci taron.
A madadin babban sakataren MDD, mataimakiyar sakataren sashen kula da harkokin siyasa, da tabbatar da zaman lafiya na MDD Rosemary A. DiCarlo ta yi godiya ga kasar Sin saboda shugabantar muhawarar. Ta nuna cewa, a bisa kokarin kasashe daban daban na Afirka, da kungiyoyin kasa da kasa da kuma MDD, an samu ci gaban yanayin tsaron a Afirka. Amma, duk da haka har yanzu ana fuskantar ta'addanci da tsattsauran ra'ayin a nahiyar, da kalubalolin dake kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da batun kare hakkin bil Adama, da doka da oda da makamantansu. Ta bayyana cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan nahiyar Afirka wajen yaki da ta'addanci, da kokarin da take na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, kana za ta tallafawa mutanen da tasirin ta'addanci ya shafa.
"Zan yi amfani da wannan dama don tuna da dubun dubantan wadanda suka yi hasara sakamakon ta'addanci a nahiyar Afirka, da nuna goyon baya ga gwamnatoci da jama'arsu da wannan matsala ta shafa. Ta'addanci yana haddasa babbar illa na dogon lokaci, don haka, ba kawai akwai bukatar a kiyaye muradun wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka tsira da ransu ba, har ma akwai bukatar a taimake su ta fannin shari'a da nuna musu goyon baya ta hanyar inganta rayuwarsu"
A yayin da suke jawabi, mahalarta taron sun yi godiya ga kasar Sin saboda shawarar da ta gabatar na shirya taron, sun kuma nuna cewa, ta'addanci bai san iyakar kasa ba, kana tsattsauran ra'ayi da ta'addanci na karuwa, wadanda suka kawo kalubale ga nahiyar Afirka da ma duniya baki daya. A don haka, ya kamata bangarori daban daban su hada kai don kawar da ta'addanci.
A nasa bangare, wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD, Zhang Jun ya bayyana cewa, ta'addanci abokin gaban daukacin bil Adama ne. Yanzu ana fuskantar yanayin yaki da ta'addanci mai tsanani. A yayin da ake fuskantar kalubale na ta'addanci, kasashe daban daban suna da makomar bai daya, babu kasar da za ta iya kare muradunta ita kadai.
"A matsayinta na wani babban yanki mai boyayyen karfi, a 'yan shekarun nan nahiyar Afirka ta fuskanci mummunar illa, sakamakon ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, abin da ya sanya ta zama a kan gaba a duniya wajen kokarin tinkarar ta'addanci. Kungiyoyin ta'addanci suna yin amfani da tashin hankali da ke faruwa a wasu yankunan Afirka, don kara bazuwa a nahiyar, da neman gurgunta zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al'ummar nahiyar, ta yadda hakan zai yi tasiri ga zaman lafiya da tsaron duniya."
Zhang Jun ya jaddada cewa, kamata ya yi a tsaya kan ma'aunin bai daya da ra'ayin bai daya a yayin da ake yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a nahiyar Afirka, da bullo da manufofi na bai daya, don kawar da su baki daya, bisa shugabancin nahiyar Afirka, da girmama 'yancinta, kana kungiyoyin nahiyar su taka rawa, don hada kai wajen yaki da ta'addanci.
Baya ga haka, Zhang ya ce, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen duniya, don nuna goyon baya da taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, don ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasuwar Afirka.
A wannan rana kuma, kwamitin sulhu ya zartas da sanarwar shugaba kan batun na zaman lafiya da tsaron Afirka. (Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China