Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata maaurata su dinga duba wayar junansu?
2020-03-11 08:55:34        cri


A cikin wannan sabon shiri na Duniyarmu A Yau, baki wadanda suka halarci tattaunawa sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batun ko "Ya kamata ma'aurata su dinga duba wayar junansu?" inda Hajiya Hauwa Ibrahim Bello da malam Yahaya Babs suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai.

A ganin Hauwa, shi soyayya tsakanin namiji da mace yadda ne, idan ban yarda da kai ba ba zan soka ba, haka kai ma ba za ka so ni ba. A waje daya, idan akwai soyayya babu alamar nuna rashin yarda a tsakani, zai duba wayata zan duba nashi.

Sannan, Hajiya Hauwa ta kara da cewa, dole ne ma'aurata su duba wayar juna ko saboda mu'amala da suke da mutane a waje, kamar a ce mu'amalar namiji da mutanen banza ko mace da mazan da ba nata ba. Bugu da kari yana da mahimmancin sanin halin da miji da mace da za ka aura ko za ki aura yake ko take ciki.

Amma a ganin Yahaya Babs, maza ba sa so a taba musu waya saboda tunanin mata sun dauke shi wajen boye sirri ne. Sannan maganin kar a yi kar a fara, babu amfanin duba wayan juna. Bugu da kari, ba'a kama mutum da laifin furucinsa, sai abun da ya kudurta.

Daga karshe dai, malam Yahaya Babs ya ce, shi idanu abun da aka boye shi yake nema, saboda haka gara kada a taba waya balle rai ya baci.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China