![]() |
|
2020-03-09 16:44:24 cri |
Bayanai na nuna cewa, tun bayan Tsai Ing-wen ta hau kan mukamin jagorar yankin Taiwan, ya zuwa yanzu, akwai kasashe guda 7 da suka kashe dangantakar diflomasiyya tsakaninsu da yankin Taiwan, sun kuma kulla dangantakar diflomasiyya da jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Lamarin da ya nuna cewa, manufar "kasar Sin kasa daya tak" ita ce ka'idar da jama'a da ma al'ummomin kasa da kasa suka yi na'am da ita.
Batun yankin Taiwan batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma batu ne da ya shafi muradun kasa. A shekarar 2018 da shekarar 2019, sassan da abin ya shafa da ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin da sauransu suka fitar da manufofin taimakawa yankin Taiwan, inda suka jaddada cewa, tabbas al'ummomi da kamfanonin yankin Taiwan za su sami damammakin raya harkokin yankin, wadannan manufofi kyawawan manufofin ne da za su taimaka matuka ga bunkasuwar yankin baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China