2020-03-09 11:40:42 cri |
A safiyar ranar 8 ga wata, firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte ya sa hannu kan wata doka, da ke sanar da killace babban yankin Lombardia da wasu larduna 14 a sauran yankuna guda hudu na kasar Italiya. Kasar Italiya ita ce kasa ta biyu bayan kasar Sin, wadda ta dauki matakan hana zirga-zirgar mutane a wuraren dake fama da cutar mai tsanani.
Haka zalika kuma, kasashen Koriya ta Kudu da Iran da wannan cuta ta bulla a kasashensu, su ma sun koyi wasu fasahohin kasar Sin.
Kwanan baya, shugaban tawagar masanan da hukumar kiwon lafiyar WHO ta turawa kasar Sin, kana, mashawarcin shugaban hukumar WHO Bruce Aylward ya bayyana cewa, matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 sun kasance abin koyi ga kasa da kasa. Da an yi amfani da fasahohin kasar Sin, da babu bukatar da sauran kasashe su fara aikin yaki da annobar daga tushe. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China