Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gaisuwa ga daukacin mata a bikin ranar mata ta duniya a wannan lokacin musamman na yaki da cutar numfashi ta COVID-19
2020-03-10 15:22:40        cri

Ko shakka babu, bikin ranar mata ta kasa ta kasa na wannan shekara, ya sha bamban da na shekarun da suka gabata. Bullar cutar numfashi ta COVID-19 a farkon wannan shekara, wadda yanzu haka ta watsu zuwa wasu sassa na duniya, ta kawo illa ga daukacin bil Adam. Amma, sakamakon wannan annobar, mun ga wasu matan da suka fito daga bangarori daban daban, wadanda suke amfani da kwarewarsu, ko mukaminsu, don taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da labarum wadannan mata.

 

 

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin taron koli na mata na kasa da kasa,

"A yayin da Sinawa ke kokarin jin dadin zaman rayuwa, ko wace mace tana da damar gudanar da ayyuka don cimma burinta. Kasar Sin za ta ci gaba da martaba babbar manufar cimma daidaito a tsakanin maza da mata, da taimakawa mata wajen taka muhimmiyar rawa, kana da ba su goyon baya a fannonin raya sana'o'insu, da tabbatar da ganin sun cimma burinsu na rayuwa."

A yanzu haka, matsayin matan dake nan kasar Sin na kara karuwa, kuma suna ta kara taka rawa a cikin al'umma, musamman ma a yayin da ake tinkarar wasu manyan hadurra, kamar matsalar da har yanzu kasar ke fuskanta ta yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Yanzu ga labarun wasu daga cikinsu.

Sakamakon yanayin annobar, dukkan makarantun dake fadin kasar Sin sun yanke shawarar jinkirta lokacin fara zangon karatu. Batun ba da ilmi, muhimmin aiki ne dake jawo hankulan dubun-dubatan iyalai a nan kasar Sin. Domin kawar da tasirin da annobar ka iya yiwa dalibai kan harkokinsu na karatu, hukumomin ba da ilmi na kasar Sin sun bullo da matakin koyarwa ta yanar gizo a yawancin yankunan kasar, saboda wannan wani sabon fanni ne da aka gwada a fannin ba da ilmi, don haka akwai bukatar malamai su kara kokarin da ba a taba ganin irinsa ba kan wannan aiki.

Zhang, malama ce dake koyarwa a wata makarantar sakandare dake birnin Beijing, ta gaya mana cewa,

"Bisa umurnin makarantarsu, za ta soma tsara darusa na musamman ne mako daya kafin a soma koyarwa, an yi haka ne don tabbatar da cewa, ba a dakatar da karatu ba duk da cewa an dakatar da lokacin komawa makaranta."

 

Malama Zhang

 

Malama Zhang ta ce, ko da yake tana fama da aiki sosai, kafin ta saba da wannan sabuwar hanya ta zamani wajen ba da darussa, amma tana ganin dalibanta suna fahimta yadda ya kamata sakamakon share fagen da ta yi, tana ganin cewa, abubuwan da ta yi sun dace, ta ce,

"Na yi imanin cewa, bayan wannan yanayin annobar, yaran za su kara imani da kan su. Kuma dukkan Sinawa za su cimma duk wani buri da suka sanya a gaba gami da kyakkyawan fata kan makomarsu. "

Malama Liang, mace ce mai kulle, mijinta likita ne a wani babban asibitin dake birnin Yantai na kasar Sin, ta gaya mana cewa, bayan bullar cutar numfashin, yawancin Sinawa na zaune ne a gida kamar yadda gwamnati ta ba da shawara, amma a matsayinsa likita, mijinta yana ci gaba da aiki kamar kullum, don haka ta damu sosai da lafiyar mijinta. Ta ce, saboda har yanzu babu maganin cutar numfashin ta COVID-19, don haka, dole ne ta yi kokarin karfafawa mijinta gwiwa kan aikin da yake na yaki da wannan cuta .

"A matsayi na na matar likita, abun da nake iya yi a yanzu shi ne, na kara mayar da hankali kan dafawa mijini abinci mai kyau da zai samu isassun sinadarai masu gina jiki, da yadda zai samu karfi da lafiya wajen gudanar da aikinsa. Ya kamata na yi kokarin tabbatar da lafiyar jikinsa."

 

Malama Liang

 

Malama Liang ta ce, a yayin da ake yaki da annobar, abun da ya fi damun ta shi ne, a farkon bullar cutar, wata rana bayan mijinta ya komo gida daga aiki, ya gaya mata cewa, ya gabatar da bukatun tafiya birnin Wuhan don ba da tallafin yakar annobar, don haka, akwai yiwuwar ya tashi zuwa Wuhan a duk lokacin da aka bukace shi. Tana jin haka, ta tsorata sosai, kuma ta kara damuwa kan mijinta. Domin ya kwantar da hankalinta, sai mijinta ya ce, "tinkarar annobar tamkar yaki ne, ko kina fatan na zama sojan da ya tsere daga yaki?" Malama Liang ta ce,

"Wannan tambayar da ya yi min, wato 'ko kina fatan na zama sojan da ya tsere daga yaki?' ta burge ni sosai, da jin haka sannu a hankali sai na kwantar da hankali, har na iya fuskantar wannan annoba yadda ya kamata."

Malama Yin, 'yayanta uku ne sakamakon yanayin annobar, yayanta ba su iya tafiya makaranta ba, don haka nauyi ya kara karuwa mata.

'Danta na farko zai yi jarrabawar shiga makarantar sakandare a watan Mayun na bana, don haka ba shi da lokaci. Ta ce,

"A matsayi na na mahaifiyarsa, dole ne na samar masa wani muhalli mai kyau na yin karatu, da dafa masa abinci masu gina jiki sosai, da kuma raka shi wajen motsa jiki da dai sauransu."

Malama Yin da diyarta

 

Malama Yin ta ce, game da 'danta na biyu yana aji na biyu a firamare, makarantar sa tana ba su darasi ta yanar gizo, saboda karami ne, wasu ayyukan gida da aka ba shi a makaranta, ba zai iya da kansa ba, don haka kullum tana taimaka masa. 'Yarsa ba ta kai shiga makarantar reno ba, don haka, ko shakka babu, tana kula da ita kusan ko da yaushe. Lallai, tana fama aiki sosai. Amma, duk da haka ta ce,

"A matsayina na mahaifiyar yara guda uku, hakika aiki ya yi min yawa a ko wace rana, amma na gamsu da irin halin da nake ciki, saboda ina son yaya na sosai."

Gaskiya mata a bangarori daban daban suna taka muhimmiyar rawarsu wajen yakar cutar numfashin ta hanyoyi daban daban da suka samu kansu.

Yanzu, bari mu leka batun malama Liang, kafin mu kawo karshen shirinmu na yau,

"Wannan lamarin gaggawa da ya faru ba zato ba tsamani, a matsayi na ta mace, na kara fahimtar ma'anar zaman rayuwa, wato akwai kasa akwai kuma gidanmu, sai kasa tana cikin lafiya, kafin mu samu lafiya a gidanmu, sannan kowanenmu zai iya jin dadin zaman rayuwa."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China