![]() |
|
2020-03-08 20:25:35 cri |
A wannan rana ta yau shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon jinjina ga masu aikin jinya mata wadanda ke gudanar da aiki a cikin asibitoci da sauran matan kasar dake taka rawa a sauran bangarori, inda ya yabawa kokarin da suke na aikin yaki da annobar.
Shugabar kungiyar mata ta duniya Nila Bayyas ta bayyana cewa, a kasar Sin, masu aikin jinya mata, likitoci ko nas suna aiki ba dare ba rana, haka kuma suna aiki ba tare da la'akari da lafiyar kansu ba, ba za a manta da babbar rawar da suke takawa ba.
Hakika kasar Sin tana aiwatar da manufar daidaiton jinsi, babu bambanci tsakanin matsayin mace da namiji, a cikin shekaru sama da 70 da suka gabata, wato tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, fitattun mata a bangarori daban daban sun yi yawa, misali kwararriya a fannin kimiyya Tu Youyou wadda ta taba samun lambar yabon Nobel da 'yar saman jannati, mace ta farko a kasar Sin wadda ta shiga sararin samaniya Liu Yang da sauransu, ko shakka babu sun taimaka kan ci gaban zamatakewar al'ummar kasar Sin, haka kuma sun gaskata ci gaban aikin kiyaye hakkin dan Adam a kasar.
Amma a wasu kasashe, ba a tabbatar da daidaiton jinsi ba tukuna, a don haka ya kamata a kara hada kai, saboda idan ba a samu ci gaban mata ba, to ba zai yiwu a samu ci gaban dan Adam ba.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China